Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Ta Ƙasa INEC, ta ce cigaba da yiwa mutane rijistar kaɗa kuri’a da ake yi a ƙasa baki ɗaya za a dakatar da shi na wucin gadi kwanaki 60 kafin babban zaɓen ƙasa na shekarar 2019.
Hukumar cikin wata sanarwa da Solomon Soyebi, kwamishina a hukumar dake shugabantar kwamitin sadarwa da kuma ilimantar da masu kaɗa kuri’a ya fitar ranar Laraba a Abuja, ya ce za a dakatar da shirin ne saboda sauyi da aka samu a dokar zaɓe.
Soyebi ya bayyana cewa ya zuwa yanzu ƴan Najeriya sama da miliyan huɗu aka yiwa rijistar a ƙasa baki ɗaya ƙarƙashin shirin da aka fara ranar 27 ga watan Afirilun shekarar 2017.
” Shirin na cigaba da yin rijistar masu kaɗa kuri’a a duk ƙasa baki ɗaya zai bawa dukkanin ƴan Najeriya da suka cancanta,masu shekara 18 zuwa sama waɗanda basu yi rijista ba a shirin da aka yi a baya damar yi a yanzu.
” Ya zuwa ya yanzu sama da mutane miliyan huɗu aka yiwa rijistar a duk faɗin ƙasar nan.
“Amma kamar yadda yake a sashi na 9 ƙaramin sashi na 5 na dokar zaɓen ƙasa ya bayyana cewa za’a dakatar da cigaba da yiwa mutane rijista kwanaki 60 gabanin babban zaɓen ƙasa wanda aka shirya gudanarwa cikin watan Faburairun 2019.
“Za a cigaba da shirin bayan an kammala zaɓen.”