Iniesta zai bar Vissel Kobe bayan shekara biyar a kungiyar



 Andres Iniesta

Asalin hoton, Getty Images

Tsohon dan wasan Barcelona, Andres Iniesta zai bar Vissel Kobe, bayan kaka biyar da kungiyar da ke buga babbar gasar tamaula ta Japan.

Mai shekara 39 zai buga wa kungiyar wasan karshe ranar 1 ga watan Yuli a lokacin da ake tsaka da gasar lik ta Japan.

Iniesta, wanda ya shiga karawa uku a canjin ‘yan wasa a kakar nan, bai yi niyar barin Vissel, wadda ta ke ta daya a kan teburi haka da gaggawa ba.

”Na so na kammala kunshin kwantiragin da ta rage min, sannan na fuskanci kalubalen da ke gaba,” in ji Iniesta.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like