Injiniyoyi A Nijeriya Sun Kirkiro Injin Samar Da Hasken Wutar Lantarki Wasu injiniyoyi a Nijeriya a karkashin jagorancin tsohon Ministan Hasken Wutar Lantarki, Farfesa Chinedu Nebo sun Kirkiro injimin samar da hasken wutar lantarki wanda aka hada shi da kayayyakin da ake samarwa a cikin gida.
Da yake karin haske kan aikin, Farfesa Nebo ya ce, an Kirkiro injin din ne ta yadda za a rage amfani da man desel wanda kuma a cewarsa, shi ne mafi zama na zamani a duk fadin duniya.

You may also like