Innalillahi Wa Inna Ilaihir Rajiun: Dan Luwaɗi Ya Halaka Wani Yaro A Kwantagora


Daga kasa hoton wani yaro kenan marigayi  Aminu da wani mutum mai suna Abubakar Maishayi wanda ake zargi da garkuwa da shi na tsawon lokaci tare da yi masa luwaɗi wanda hakan ya yi sanadiyyar rasa ransa.

Al’ummar karamar hukumar Kontagora da kewaye sun nuna matuƙar ɓacin ransu tare da kira ga hukumomi da su gaggauta bi wa wannan yaro hakkinsa.
Allah ya jikansa da rahama, Allah ya kuma ya shiryi masu aikata wannan mummmar dabi’a.
Shin a ra’ayin ku wani irin hukuncin ya dace a rika yiwa masu aikata Fyaɗe  da Luwaɗi   musamman ga kananan yara a Nijeriya?

You may also like