Majalisar Najeriya ta tara marasa gaskiya-Obasanjo


Tsohon shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya caccaki majalisar tarayyar kasar, inda ya bayyana mambobinta a matsayin marasa gakiya da rikon amana.

Kalaman tsohon shugaban na zuwa ne sakamakon zarge-zargn da ake yi wa mambobin majalisar wakilai na kokarin shigar da cuwa-cuwa a kasafin kudin shekara ta 2016.

Obasanjo wanda ya bayyana haka bayan ya gana da shugaban kasar Muhammadu Buahri a birnin Abuja a jiya, ya ce, an wayi gari a yau, inda majalisar ta tara marasa gakiya.

A makon jiya ne, tsohon shugaban kwamitin kula da kasafin kudi na majalisar wakilai, Abdulmimin Jibrin ya caccaki shugaban majalisar Yakubu Dogara da mataimakinsa, Yusuf Suleiman da mai tsawatarwar majalisar, Alhassan Ado Doguwa da kuma shugaban marasa rinjaye Leo Ogor kan yadda suka yi kokarin tirsasa masa shigar da ayyukan da za su lakume kimanin Naira biliyan 40 a cikin kasasfin.

Sai dai ana zargin cewa sun yi kokarin cika aljihunsu da kudaden ne kawai ba tare da gudanar da wani aiki ba.

Obasanjo ya ce, ya kamata shugaba Muhammadu Buhari ya sa ido sosai kan sha’anin majalisar wadda ya ce, “ta tara barayi.”

Tuni dai wasu daga cikin ‘yan majalisar tarayyar suka fara mayar wa da Obasanjo martani kan kalamasa.

You may also like