
Asalin hoton, Getty Images
Inter ta koma matsayi na hudu a Serie A da tazarar maki takwas tsakaninta da Napoli ta daya
Kwallo daya da Edin Dzeko ya ci da kai ta taimaka wa Inter Milan ta koma matsayi na hudu a gasar Serie A.
Wannan ce rashin nasarar farko ga Napoli da ke matsayi na daya a gasar, cikin wasa 16 da aka yi ya zuwa yanzu, wadda kuma ke da maki 41.
Inter ta koma saman Lazio da maki uku, bayan kashin da Lazio ta sha a hannun Lecce da ci 2-1.
A minti na 56 ne da fara wasan Dzeko ya ci kwallon wadda Federico Dimarc ya kwaso daga gefe.
Mai tsaron ragar Inter Andre Onana ya hana kwallon da Giacomo Raspadori ya buga na kusa tashi daga wasan, hakan ya kawo karshen nasarar da Napoli ta samu 11 a jere a Serie A.
Ba dan wannan rashin nasara da ta yi ba, da Napoli ta bayar da tazarar maki takwas da ga Ac Milan da ta yi nasara a jiya.