Inuwa Yahaya ya lashe zaɓen gwamnan jihar Gombe karo na biyuInuwa Yahaya

Hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC ta ayyana Inuwa yahaya na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar.

INEC ta bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a kan abokan hamayyarsa Muhammad Jibri Ɗan Barde na jam’iyyar PDP da kuma Ahmed Khamisu Mailantarki na jam’iyyar NNPP.

Babbar jami’iar tattara sakamakon zaɓen jihar Farfesa Maimuna Waziri ta ce Inuwa ya samu nasara da ƙuri’u 345,821.

Shi kuwa Ɗan Barde na PDP ya samu ƙuri’a 233,131, yayin da Mailantarki na NNPP ya zo na uku da ƙuri’u 19,861.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like