IOM: ‘Yan gudun hijira 366 ne suka mutu a tekun Mediterrenean a 2017


56e96a4425b67

 

 

 

Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, a watanni 2 na farkon shekarar 2017 ‘yan gudun hijira 366 ne suka rasa rayukansu a a tekun Mediterrenean a yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa kasashen Turai.

Wannan adadi ya ragu kasa da na watanni biyun farkon shekarar 2016 wanda ya kama mutane 425.

Sanarwar da Hukumar ta IOM ta fitar ta ce, ‘yan gudun hijira dubu 13,427 sun shiga Turai ta teku wanda ya ragu sosai a irin wannan lokaci a shekarar da ta gabata wanda ya kama mutane dubu 105,427.

Wannan adadi na wadanda suka mutu ya hada da na wasu mutane 133 da suka mutu a Al-Zawiyah da ke kusa da Tarabulus.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like