Iraki: An halaka ‘yan ta’adda masu yawa a birnin Musel.


 

Ma’aikatar tsaron Iraki ta sanar da kashe ‘yan kungiyar Da’esh da dama a gabacin birnin Musel.

Ma’aikatar tsaron Iraki ta sanar da kashe ‘yan kungiyar Da’esh da dam aa gabacin birnin Musel.

A wani bayani da ma’aikatar tsaron ta Iraki ta fitar ya kunshi cewa; A ci gaba da kokarin korar ‘yan ta’addar Da’esh daga birnin na Musel, sojojin kasar sun kwace kauyukan alqusiyat da wasu garuruwan da su ke kusa da Musel.

Bayanin ya kuma kunshi cewa; Sojojin kasar sun kuma kashe ‘yan ta’adda 50 da kuma lalata wasu motoci 6 da aka makare da maba-bamai, haka nan kuma rushe wata masana’anta ta makamai.

sojojin na Iraki sun kuma yi nasarar kwace gabacin birnin Musel daga ‘yan ta’addar ta Musel.

You may also like