Iraki : An kai hari a Bashika


57fa33910cc3c

Kungiyar ‘yan ta’ddan Daesh sun kai hari a yankin Bashika na gabashin Iraki.

Bayan harin da suka kai sun fafata da sojojin.

Rahotanni sun ce, a yayin kai harin an mauaywar da Daesh din martani inda aka harba musu wani babban makami amma kuma babu abinda ya samu ‘yan ta’addar da ke cikin tankar yakin.

Bayan mayar da martanin motar ta canja wuri inda wani makami da aka harba ya kuma fada kan ginin da ‘yan ta’addar suke ya yi sanadiyyar mutuwar ‘yan ta’addar su 10.

Wasu karin ‘yan ta’adda da dama sun mutu yayinda aka kai musu hari a lokacinda suke kokarin guduwa daga yankina a cikin motoci guda 4 da kuma babura.

Haka zalika an kai hari a wasu wurare da aka gano Daesh na zaune a yankin.

You may also like