Iraki : An Kashe ‘Yan Ta’adda 900 A Mosul


 

Wani janar na sojin Amurka ya ce an kashe ‘yan ta’addan IS kimanin 900 a farmakin da ake ci gaba da kaiwa na kwato yankin Mosul na Iraki.

Saidai a cewar Janar, Joseph Votel, mahukuntan Iraki sun sanar masu da mutuwar sojojin kasar 57 da kuma wasu 255 da suka raunana.

Ko baya ga hakan mayakan Kurdawa dake tallafawa dakarun Irakin sun rasa mayakansu 30 zuwa 70 da kuma wadansu akalla 100 da suka raunana.

Kawo yanzu mutane 12,000 ne zuwa 15,000 sukayi kaura a yankin a farmakin da dakarun Irakin ke kaiwa da nufin tsarkake birnin dake zamen na biyu mafi girma a Iraki.

Yau kusan kwanaki 12 kenan da dakarun Iraki haddin gwiwa da mayakan sa kai na ‘yan shi’a wadanda ke samun tallafin kawancen da Amurka ke jagoranta suka som akai farmaki a yankin na Mosul dake zamen tungar karshe ta ‘yan ta’addan IS a kasar ta Iraki.

You may also like