Iran ta aike da jiragen sama guda biyar dauke da kayan abinci zuwa kasar Qatar, wadda take fama da rashin abinci bayan makwabtanta sun rufe iyakokinsu da ita.
A makon jiya ne kasashe da dama suka yanke mu’amala da Qatar ciki har da Iran- wadda ba ta ga maciji da Saudiyya, bisa zargin kasar da goyon bayan ayyukan ta’addanci, Zargin da Qatar din ta musanta.
Saudiyya ta rufe iyakarta da Qatar, wadda kaso 40 cikin 100 na abincin da Qatar take samu yake shigowa daga nan.
Hakazalika, an umarce ‘yan kasar Qatar da suke zaune a wasu kasashen Larabawa da su fice, sai dai ita Qatar ba ta dauki irin wannan matakin ba tukuna.
A ranar Lahadin nan ne mai magana da yawun kamfanin jiragen saman Iran, Shahrokh Noushabadi, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Agence France-Presse cewa:
“Zuwa yanzu akwai jirage guda biyar da suke dauke da kayan abinci da ‘ya’yan itatuwa da aka tura kasar Qatar, kowane jirgi yana dauke da kimanin tan 90 na abincin, yayin da za a kara aikewa da wani jirgin a yau.
“Sai dai ba a san ko wannan wani taimakone na jinkai ba, ko kuma wani cinikin kasuwanci ne tsakanin kasashen biyu.
Kamfanin Jirgin Saman Iran ya wallafa a shafinsa na Twitter hoton jiragen sama ana loda musu kayan abinci a filin jirgin saman Shiraz.
Mista Noushabadi ya ce za su ci gaba aike wa da kaya Qatar “idan akwai bukatar hakan”.
Har ila yau, kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce akwai jiragen ruwa guda uku wadanda suke dauke da tan 350 na kayan abinci da Iran za ta tura Qatar.
Hakazalika, Iran ta bai wa jiragen saman Qatar izinin amfani da sararin samaniyanta, bayan Saudiyya da Bahrainda kuma Hadaddiyar Daular Larabawa sun hana ta amfani da nasu.