Iran Ta Jajantawa Kasar Rasha Akan Hatsarin Jirgin Sama


4bk9cb6e897a1bd961_800c450

 

Kakakin Ma’aikatar Wajen Iran ya jajantawa Kasar Rasha saboda fadowar jirgin kasar a tekun Balck Sea.

Bahram Qasimi ya ce muna mika sakon ta’aziyya ga gwamnati da al’ummar kasar Rasha, saboda mutuwar mutane 90 da jirgin Topolov 154 ya fado da su a cikin tekun Black Sea.

A yau lahadi ne ma’aikatar tsaron kasar Rasha ta sanar da cewa; Jirgin sama samfurin Topolov 154 ya fado a tekun Black Sea jim kadan bayan tashinsa daga filin saukar jiragen sama na Sochi.

Jirgin dai yana kan hanyarsa  ne ta zuwa Lazikiyya na kasar Rasha dauke da masu kidan Coir, domin halartar bikin kirsimeti tare da sojojin Rashan.

You may also like