Iran ta nemi Saudiyya data daina yada kiyayya da take Hakki


Shugaban Iran Hassan Rouhani

Shugaban Iran, Hassan Rouhani ya yi kira ga babbar abokiyar hamayyar kasarsa a yankin Larabawa, Saudiyya, da ta daina take hakki da kuma yada akidar kyamar kasashe masu makwabtaka da ita.
Rouhani ya yi wannan kiran ne a babban taron Majalisar Dinkin Duniya, a inda ya ce hakan ne kawai zai tabbatar da cewa Saudiyyar da gaske take yi wajen samar da tsaro da cigaba a yankin.

Shugaban ya kuma kara da yaba wa kasar tasa dangane da habakar tattalin arzikin da ta samu watannin takwas da suka gabata sakamakon cire mata takunkumin da aka kakaba mata kan shirinta na nukiliya.

Sai dai kuma Rouhani ya caccaki Amurka kan abin da ya kira jan kafa wajen kammala cire mata takunkumin gaba daya.

You may also like