Iran Ta Yi Allawadai Da Harin Da Aka Kai A Garin Madagali Na Jahar Adamawa Najeriya


 

 

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana hare-haren da aka kai a garin Madagali na jahar Adamawan tarayyar Najeriya da cewa aiki ne na ta’addanci, wanda ya kamata a yi tir da Allawadai da shi.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran Bahram Kasimi ya ce; Iran tana yin Allawadai da wanann hari na rashin imani da aka kai a Madagali, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula da ba su san hawa ba, ba su san safka ba, suna neman abin da za su saka  a bakin salatinsu tare da iyalansu.

Ya ce gwamnatin kasar Iran na nuna alhininta ga gwamnati da kuma daukacin al’ummar Najeriya musamman ma iyalan wadanda abin ya rutsa da su.

Kasimi ya ce abin da ya faru a garin Madagali daidai yake da sauran ayyukan ta’addanci da ‘yan ta’adda suke aikatawa a sauran kasashen yankin gabas ta tsakiya da sauran kasashen duniya, wanda hakan ke nuni da irin wajabcin hada karfi da karfe tsakanin dukkanin kasashe domin ganin bayan mummunar akida ta kafirta musulmi da yi musu kisan gilla da sunan jihadi.

You may also like