Iran: Ya Kamata Malaysia Ta Yi Taka Tsantsan Domin Kada A Hada Ta Fada Da Musulmi


 

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Bahram Kasimi ya kirayi gwamnatin kasar Malaysia ta yi taka tsatsan matuka dangane da hankoron da ake yi na jefa ta cikin fada da wani bangaren musulmi.

Bahram Kasimi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake mayar da martani a kan bayanin karshe na ziyarar sarkin masarautar Ali-Saud Salam bin Abdulaziz a Malaysia, wanda bayani ne na hadin gwiwa tsakanin Malaysia da masarautar Ali-Saud.

 

Bayanin nasu ya zargi gwamnatin Iran da shiga cikin harkokin kasashen yankin gabas ta tsakiya, a kan haka Bahram kasimi ya bayyana cewa, kasarsa ba ta tsoma baki a cikin harkokin wata kasa, amma dai tana aiki kafada da kafada tare da wasu gwamnatoci a yankin domin yaki da ayyukan ta’addanci, wanda kuma tabbas hakan ba zai yi masu daukar nauyin ayyukan ta’addanci dadi ba.

Kasimi ya ce a matsayin Malysia na babbar kasa ta musulmi da ake ganin kimarta, bai kamata ta zama tamkayar kayan wasa a hannun wasu ba.

 

 

Kasimi ya yi ishara da cewa a kwanakin baya an gudanar da zaman taron kasashen musulmi a Malaysia domin daukar matakai na kare rayukan musulmin kasar Myanmar da ake zalunta, wanda kuma kasar Iran ce ta dage domin ganin an gudanar da taron, haka nan kuma ita ce ta taimaka ma Malaysia domin daukar bakuncin taron, Kasimi ya ce irin wadannan ayyukan na hada kasashen musulmi su ne ne abin da ya kamata Malaysia ta mayar da hankali a kansu, kada ta amince da duk wani abun da zai kara jawo rarraba kan musulmi da kawo fitina da rikici a tsakaninsu, domin hakan kwangila ce ta yahudawa da ‘yan mulkin mallaka da suka baiwa wasu daga cikin kawayensu musulmi domin aiwatar da ita, da nufin raunana kasashen musulmi musamamn a yankin gabas ta tsakiya, suna tura ‘yan ta’adda suna kashe musulmi da tayar da bama-bamai da sunan jihadi, suna kashe mata da kanan yara Yemen, a lokaci guda kuma suna tuhumar Iran da cewa tana tsoma baki a harkokin kasashen yankin.

You may also like