
Mutanen da aka kasa ganewa bayan kashe su a Izyum na jibge a cikin wata kwantena da ke Kharkiv
Oleh Podorozhnyy ne ke jagorantar mutane zuwa mutuwarensa mai duhu wadda buhuhunan yashi suka toshe tagunanta.
Da zarar an buɗe ƙofofinta na ƙarfe masu nauyi, sai warin gawarwaki ya bigi hancin mutum.
Kwantenar cike da tudun gawarwakin mutanen da aka kashe lokacin da garin Izyum ke hannun Rasha. Da yawan gawarwakin sun shafe watanni.
Ana yi wa jikkunan lamba da kuma taƙaitaccen bayani cikin baƙin rubutu. Makwanni bayan sake ƙwato Izyum ɗin, har yanzu ba a tantance sunayen mutum 146 da aka tarar a garin ba.
An kawo su nan ne saboda babbar mutuwaren cike take maƙil da gawarwarkin da ba a tantance ba da aka kashe sakamakon harin makamai masu linzami na Rasha.
“Adadin mutanen da ba mu tantance ba suna da yawa sosai,” a cewar Oleh, wani mai bincike cibiyar bincike ta Kharkiv Bureau of Forensic Expertise.
“Za su ci gaba da zama a nan yayin da ake kammala gwajin DNA.”
Nema kamar ba za a samu ba
Ana iya ganin ɓarnar da Rasha ta yi a garin Izyum mai yawan gaske.
Wani dogon rukunin gidaje ya fuskanci luguden wuta har sai da aka yi wani rami a tsakiya da kuma gefensa, wasu gidajen na gefensa kuma sun zama ɓaraguzai.
Akwai kuma iyalai da ke zaune cikin wannan yanayi kuma suke ci gaba da neman ‘yan uwansu da suka san an kashe su amma ba su ga gawarsu ba.
An lalata ofishin ‘yan sanda na Izyum, saboda haka ‘yan sandan suka kafa wata cibiyar karɓar samfurin halittar mutane a wata kwaleji.
Hukumomi na karɓar samfurin danshin bakin mutane don gano ‘yan uwansu da aka kashe
Akan kira mutane ɗaya bayan ɗaya kuma a ɗauki danshin bakinsu. Sai a tura shi ga wata cibiya da za ta ciri ƙwayar halittar DNA da zimmar gano mai irin wannan samfurin a cikin gawarwakin mutanen.
Baya an ɗauki nata samfurin, Tetyana Tabakina ta tsaya a tsakiyar ɗakin da hannunta a baki cikin alhini.
An kashe ‘yar uwarta Iryna, da ɗan ‘yar uwarta Yevheniy a hare-haren Rasha a gidansu a watan Maris. Yanzu suna zaune a gidan ƙasa, inda suke ganin ya fi aminci.
Tetyana ta samu damar gane Yevheniy saboda wani zane da ke hannunsa amma har yanzu ba ta iya gano ‘yar uwarta ba.
“Ira ta ɗaiɗaice a harin. Na kasa ganin komai nata,” in ji ta cikin sanyayyar murya. “Ina jira na samu ko da ɗan wani abu ne na ‘yar uwata don na binne su tare.”
An kashe Iryna da ɗanta Yevheniy a harin Rasha a watan Maris
Wahalhalu game da gwajin DNA
Yaƙin da ya jefa Tetyana cikin wannan hali shi ne dai ke ƙara wa neman gawarwakin wahala.
Lokacin da Rasha ta mamaye Kharkiv, cikin masu guduwa har da masu binciken gano gawarwaki.
“Muna bai wa wasu horo, amma yanzu mutum takwas kawai gare mu a wannan sashen kuma aikin na nan jibge,” kamar yadda Viktoria Ionova ya bayyana.
“Akwai kuma matsalar ɗaukewar lantarki. Na’urori masu basira sai su daina aiki nan take, dole sai mun sake komai tun daga farko. Muna da jannareto, amma wani zubin mukan rasa wuta tsawon rana guda.”
Hanyoyin da wasu ke mutuwa na rikitar da masu bincike: da yawa sun ƙone sosai a hare-haren.
Hukumomi sun tono gawa kusan 900 a yankin Kharkiv
Sai dai kuma ba dukkan mamatan ne ke da ‘yan uwan da za su ba da samfuri don gano su ba.
Ƙaburbura a daji
An binne mafi yawan mutanen da aka kashe a wasu ƙaburbura a dajin da ke wajen gari.
Masu haƙar ƙabari ‘yan sa-kai ne suka binne su.
Lokacin da dakarun Ukraine suka ƙwato garin a watan Satumba, an tono gawarwakin kum aka mayar da su Kharkiv. ‘Yan sanda sun ce wasu sun mutu ne ta wasu hanyoyi, yayin da aka kashe da yawa a hare-haren Rasha.
Yanzu sun tono mutum 899 a faɗin yankin.
“Abu ne mai wuya ƙwarai. Ba mu taɓa ganin gawarwaki da yawa kamar haka ba. Tsakatsaki, muna tono gawar mutum 10 a kullum,” a cewar Serhiy Bolvinov, shugaban sashen bincike na ‘yan sandan Kharkiv.
A wannan makon jami’ansa suka gano gawar wani mutum da harin bam ya kashe kuma matarsa ta binne shi a lambun gidansu.
Jimillar gawar mutum 451 aka gano a Izyum, ciki har da yara bakwai.
“Allah ya koya mana yafiya amma ba zan taɓa yafe wa makasa ba,” in ji Olena Ihnatenko yayi jana’izar mijinta
Dogon jira
Zuwa yanzu, gawa biyar kawai aka tantance ta hanyar amfani da DNA a Izyum. Tawagar binciken ta ce wasu daga cikinsu sun lalace sosai suna fargabar ba za a iya gane su ba har abada.
A wajen Tetyana Tabakina, abin ya zama dogon jira.
Ta ce a kwanan nan wani maƙwabcinta ya binne mutum bakwai dangi ɗaya wadanda aka kashe a harin da ya halaka ‘yar uwarta.
“Ya faɗa min cewa washegarin ranar da aka binne su kamar an cire masa wani babban nauyi ne kuma sai lokacin ya fara yin barci,” Tetyana ta bayyana.
“Ina so ne kawai na ga bayan lamarin nan, ko abin ya kawo ƙarshe a wajensu cikin sauƙi ko kuma a wajenmu.”