
Asalin hoton, AFP
Kotu ta umarci a rufe fuskar hotunan Irmgard Furchner da ake shari’a
An sami tsohuwar sakatariyar da ta yi aiki da kwamandan sansanin Nazi da hannu a mutuwar sama da mutum 10, 505.
Irmgard Furchner, mai shekara 97, a lokacin da take budurwa ta yi aiki a mataayin mai buga takarda a Stutthof, inda ta yi aiki a can daga shekarar 1943 zuwa 1945.
Furchner wadda tana daya daga cikin mata da ake yi wa shari’a kan laifukan Nazi, da aka yankewa hukuncin zaman gidan yari tsawon shekara biyu.
Duk da cewar farar hula ce ma’aikaciya, alkalin ya amince cewar tana da cikakkiyar masaniyar abun da ke faruwa a sansanin.
An yi zaton wasu mutane su 65, 000 sun mutu a wani mumunan yanayi mai cike da mamaki a Stutthof, da ya hada da fursunonin Yahudawa da wadanda ba Yahudawa ba da wasu sojijin Sobiyet da suka kama.
Kasancewar Furchner na da shekara 18 ko 19 a lokacin, an mata hukunci a kotun masu karancin shekaru.
A Stutthof da ke kusa da sabon birnin Polish a Gdansk, akwai hanyoyi da aka yi amfani da su wajen kashe daurarru, kuma dubban su sun mutu ne a sashen ajiye gas a wajen daga Yunin 1944.
Kotun Itzehoe da ke Jamus ta arewa ta saurari muryoyin wadanda suka tsira a sansanin, inda daga baya aka samu wasu daga cikinsu da suka mutu a yayin da ake shari’ar.
Lokacin da aka fara shari’ar a watan Satumbar 2021, Irmgard Furchner ta tsere daga gidanta, daga bisani ‘yan sanda suka ganota a kan layin Hamburg.
An daure kwamnadan Stutthof Paul-Werner Hoppe a gidan yari a shekarar 1955, da zargin alaka da kisan, amma daga bisani aka sako shi bayan shekaru biyar.
An yankewa da dama hukuncin a Jamus tun 2011, bayan da aka yankewa tsohon mai gadin sansanin Nazi John Demjanjuk, ya zama izina na cewar zama mai gadi shi ma hujja ce ta bayar da cikkakun hujojin hannun mutum a ciki.
Hukucin na nufin cewar Furchner ma’aikaciyar wadda farar hula ce, ya dace ta tsaya a gaban kotu, saboda kai tsaye ta yi aiki kai tsaye da kwamandan sansanin, da masaniya kan halin da dauraru da ke Stutthof.
Sai da aka dauki kwana 40 kafin ta iya magana a gaban kotu, inda ta fada mata cewar “a yi hakuri kan dukkan abun da ya faru.”
“Na yi da na sanin abun da ya faru, lokacin da nake Stutthof – shi ne abun da zan iya cewa,” in ji ta.
Lauyan da ke ba ta kariya a gaban kotu ya bukaci da a wanke ta, saboda kokwanto da ya dabaibaye abun da take da masaniya akai, kasancewar ta daya daga cikin masu buga takarda a ofishin Hoppe.
Masananin tarihin Stefan Hördler ya taka rawa a shari’ar tare da wasu alkalai biyu, a wata ziyara da suka kai sansanin.
Daga ziyara da aka yi sansanin ya fito ƙarara cewar Furchner ta ga wasu daga cikin mafi munin yanayi a sansanin daga ofishin kwamanda.
Masanin tarihin ya sanar da kotun cewar motoci 27 da ke dauke da mutum 48,000 ta isa Stutthof a tsakanin Yuni da Octoban 1944, bayan da Nazi ta yanke hukucin fadada sansanin da hanzarta kisan aadadin mutane mai yawa ta hanyar amfani da nau’in gasa na Zyklon B.
Mr Hördler ya bayyana ofishin Hoppe’s da nan ne “cibiyar da ake shirya komai” da ke tafiya a Stutthof.
Asalin hoton, Getty Images
Matar Josef Salomonovic ce ta sa shi ya taho daga Vienne zuwa Jamus ta arewa don bayar da shiada a karshen Disamba
Daya daga cikin wadanda suka tsira daga sansanin Josef Salomonovic, da ya zo kotun don bayar da shaida a shari’ar, na da shekaru shida a lokacin da aka harbe mahaifinsa ga bindiga a Stutthof, a watan Satumba na 1944.
“Kai tsaye ba za a ce tana da laifi ba” ya fada wa ‘yan jarida cewar a kotu a Disambar da ya gabata, “ko da zama kawai ta yi a ofishin ta buga sitamfi a takardar a kashe mahaifi ne.”
Haka shi ma wani da ya tsira, Manfred Goldberg, ya ce abin kunyarsa daya shi ne yadda hukucin shekaru biyu da aka yi mata “ya sama kamar kuskure.”
Ya ce “babu wani mutum da ke hankalinsa da zai tura mutum mai shekaru 97 zuwa gidan yari, amma hukucin nata zai tsaurin laifukan,”.
“Idan za a yankewa wanda ya saci wani abu a shago, shekara biyu, yaya za a yanke wa mutumin da ya taimaka wajen kisan mutum 10, 000, a yi masa makamancin hukuncin?
Laifukan Nazi tun 2011
- John Demjanjuk – an dure shi a 2011 tsawon shekara biyar, na samun hannun a kisan sama da Yahudawa sama da 28, 000 a sansanin mutuwa na Sobibor, amma aka sake shi bayan jiran daukaka karar kuma ya mutu bayan zagayowar shekara yana da shekara 91.
- Oskar Gröning – “Mai ajiyar littafin Auschwitz”, an yanke masa hukuci a 2015, a masayin wanda ke da alaka da kisan sama da Yahudawa 300, 000. An aika da shi gidan yari inda ya mutu a 2018 yana da shekaru 96 yayin da ake jiran daukaka kararsa.
- Reinhold Hanning – Tsohon mai gadin SS a Auschwitz, an ayan ke masa hukucin ne kan taimaka waje kisan kiyashi a wata Yunin 2016, amma ya mutu yana da shekaru 95, yayin da shina ake saurara daukaka kararar.
- Friedrich Karl Berger – Tsohon mai gadin sansanin Neuengamme, da aka dawo da shi Jamus daga Amurka a watan Fabarerun 2021 yana da shekara 95. Masu tuhumar na kasar Jamus, sun ajiye laifukan da aka tuhumar sa akai, yanzu kuma ba a san makomarsa ba.
- Josef S – an yanke masa hukucin daurin shekara biyar a cikin watan Yunin 2022 don taimakawa wajen kisan dauraru sama da 3, 500 a sansanin Sachsenhausen. Ya kasance mai shekara 101, amma saboda yanayin rashin lafiya ya sa akwai yiwuwar ba zai yi wani zaman kurkuku ba.
Shari’ar Furchner za ta iya kasancewa ta karshe a Jamus, kan laifukan sojojin Nazi, duk da cewar akwai wasu laifuka kalilan da har hanzu ana ci gaba da bincike a kansu.
Akwai wasu laifuka biyu da tuni aka kai su gaban kotu kan zargin wasu laifuka da Nazi ta aikata a Stutthof.
A shekarar da ta gabata, sai da kotu ta dakatar da shari’ar da ta ke yi wa wani tsohon mai gadin sansanin, kan karancin lafiya, duk da cewar akwai “hasashe mai ƙarfi” da ke cewar yana da laifi na sanin yadda aka yi kisan.
A shekarar 2020, shi ma wani mai gadin sansanin Bruno Dey, da aka yanke masa hukucin shekara biyu a gidan yari bisa zargin hannu a kisan dauraru sama da 5, 000.