IS ta kashe mutane 80 a harin da ta kai a Kabul


 

Kungiyar IS da ke da’awar jihadi ta ce ita ta kai hare haren bama bamai guda biyu akan gangamin masu zanga-zanga a birnin Kabul na Afghanistan inda mutane sama da 80 suka mutu sannan sama da 200 suka jikkata.

Ma’aikatar cikin gida ta ce adadin mutanen da suka mutu na iya karuwa bayan tabbatar da mutuwar mutane 80.

An dai kai harin ne akan mabiya Shi’a a dandalin Deh Mazang a Kabul wadanda ke zanga-zangar adawa da dauke hanyar lantarki zuwa yankinsu.

Kungiyar Taliban ta nisanta kanta da harin tare da yin allawadai.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like