Asalin hoton, WHO
Makomar jariran ya shiga garari a daidai lokacin da asibitin al-Shifa ke fuskantar ƙarancin man fetur da kuma dakatar da aiki
An kwashe jarirai bakwaini 31 daga asibitin al-Shifa da ke birnin Gaza, wanda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta kwatanta da “sansanin mutuwa”.
An ɗauki jariran zuwa wani asibiti da ke kudancin birnin Rafah, kusa da iyaka da Masar.
Ɗaruruwan mutane, ciki har da marasa lafiya, suka bar al-Shifa a ranar Asabar.
Asibitin – wanda ya kasance mafi girma kuma na zamani a yankin – na karkashin ikon sojojin Isra’ila.
Sojojin na bincike domin samun shaidun cewa asibitin ya kasance a matsayin cibiyar Hamas.
A ranar Asabar aka kwashe ɗaruruwan mutane, ciki har da marasa lafiya daga asibitin, sai dai an bar wasu 300 da suke cikin tsananin ciwo, da kuma wasu bakwaini 33.
Mai magana da yawun ƙungiyar agaji ta Red Crescent ta faɗa wa BBC cewa jariri ɗaya ya mutu a yammacin ranar Juma’a da kuma wani da ya sake mutuwa a safiyar Asabar.
A ranar Lahadi, Red Crescent tare da haɗin gwiwar Majalisar Ɗinkin Duniya suka kwashe bakwaini 31 da suka tsira.
Mai magana da yawun Red Crescent ɗin Nebal Farsakh ta faɗa wa BBC cewa an kashe iyayen wasu daga cikin bakwainin a wani hari ta sama da Isra’ila ta kai.
BBC ba ta kai ga tabbatar da hakan ba.
Ta ce an bai wa iyayen da suka tsira da su fice daga birnin Gaza – wajen da asibitin al-Shifa yake – kafin a kwashe jariran, kuma ba a san inda suke ba.
Shafin Facebook na ma’aikatar lafiya ta Gaza ya buƙaci iyayen jariran da su tafi asbitin Rafah domin sake haɗuwa da ƴaƴansu.
Isra’ila ba ta ce uffan ba kan lamarin, duk da cewa a baya ta ce za ta taimaka wajen kwashe jariran zuwa wani asibitin da ba shi da haɗari.
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce jariran na cikin “tsananin rashin lafiya”, kuma an kwashe su karkashin tsauraran matakan tsaro, inda suke ci gaba da samun kulawa a sashen jarirai na asibitin Rafah.
Sun samu rakiyar jami’an lafiya shida da kuma iyaye goma, in ji shi.
A baya, likitoci a asibitin al-Shifa sun ce bakwaini sun mutu bayan ɗaukewar wutar lantarki sakamakon rashin man fetur da injunan bayar da lantarki za su yi amfani da shi.
WHO na yin wani shiri don kwashe sauran jariran da ma’aikatan lafiya daga asibitin al-Shifa da zarar an samar da hanyar fita mai sauki, in ji Ghebreyesus.
Daraktan asibitin al-Shifa Dr Muhammad Abu Salima ya yi kira ga WHO da MDD da su taimaka wa tawagar likitoci da marasa lafiya don ficewa daga “wannan wuri mai hatsari”.
Ya faɗa wa sashen Larabci na BBC cewa akwai jami’an lafiya 25 da suka rage a asibitin, sai dai babu ruwan sha da wutar lantarki, inda hakan ya janyo ba a iya bai wa ɗaruruwan marasa lafiya kulawar da ta dace.
“A yanzu, asibitin, ya zama wurin da babu kowa,” in ji shi.
“Gawawwaki na watsuwa a sashen kula da masu gaggawa, marasa lafiya na ta tsala ihu, yanayin ya fi karfin likitoci, sojoji kuma na yawo cikin asibitin ba tare jin komai ba,” in ji Dr Muhammad.
Asalin hoton, Palestinian Red Crescent
Ƙungiyar agaji ta Red Crescent ta ce an kwashe jariran ne tare da haɗin gwiwar WHO da kuma MDD
Isra’ila ta ce Hamas na da cibiya a karkashin asibitin al-Shifa – wani iƙirari da Hamas ɗin ta musanta – sai dai ba ta bayar da shaidun hakan ba.
A farkon wannan mako, mai magana da yawun sojojin Isra’ila, Laftanar Kanal Jonathan Conricus, ya ce za a ɗauki tsawon makonni kafin kammala gudanar da bincike a asibitin.
Ƙungiyar Hamas, wadda aka ayyana a matsayin ƙungiyar ta’addanci a ƙasashen yammacin duniya da dama, ta kai wa Isra’ila hari a ranar 7 ga watan Oktoba, inda ta kashe mutum 1,200 tare da yin garkuwa da sama da 240.
Isra’ila ta kaddamar da wani gagarumin farmaki na ramuwar gayya – wanda ya haɗa da hare-hare ta sama da kuma harba makaman atilare – da nufin kawar da Hamas.
Ma’aikatar lafiya ta Hamas ta ce adadin waɗanda suka mutu a Gaza tun daga lokacin da yaƙi ya ɓarke ya kai 12,300.
Fiye da 2,000 ne ake fargabar an binne su a karkashin ɓaraguzan gine-gine.