Isra’ila ta kai hari Lebanon da Gaza da ta ce na ramuwar gayya ne kan ruwan makaman roka da ta zargi Hamas da yi mata.Harin da Isra'ila ta kai

Asalin hoton, AFP VIA GETTY IMAGES

Bayanan hoto,

Isra’ila ta kai harin ne a kan abin da ta ce ramuwar-gayya ta harin roka

Rundunar sojin Isra’ila, ta ce ta yi nasarar kai hare-hare kan wuraren kungiyar Hamas a zirin Gaza da kuma Lebanon.

Isra’ila ta ce hare-haren da ta kai ta sama, su ne mafiya muni tun watan Augusta.

Harin martani ga hare-haren roka da aka kai mata daga kudancin Lebanon, wanda Isra’ilar ta dora alhaki a kan kungiyar Hamas.

Hukumomin sojin Isra’ila sun zargi kungiyar Hamas da harba gomman makaman roka daga kudancin Lebanon zuwa cikin arewacin kasarsu.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like