Isra’ila ta kai munanan hari a birnin Rafah..

Asalin hoton, GETTY IMAGES

Isra’ila ta yi luguden wuta ta sama a kan garin Rafah da ke kudancin Gaza, inda Falasɗinawa fiye da miliyan ɗaya ke neman mafaka.

Mazauna yankin sun shaidawa BBC cewa an kai hari ta sama aƙalla sau 50, a tsakiyar dare.

Kakakin rundunar sojin Isra’ilan ya ce sun kuma kuɓutar da biyu daga cikin mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su a Gazar, a yayin hare-haren.

Rahotannin da suka fara fitowa daga yankin sun ce an kashe mutane fiye da ashirin.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like