Isra’ila ta kai wasu hare-hare a Labanan da Gaza | Labarai | DWHare-haren na yau Juma’a, sun zo ne dai bayan wasu rokoki da mayakan kungiyar Hamas suka harba daga yankin falasdinu, da kuma suka fada a wasu yankuna na Isra’ila a jiya Alhamis.

Haka ma an harba wasu sama da rokoki 30 daga Labanan zuwa Isra’ilar a jiya Alhamis.

Mayakan yankin na falasdinu dai sun fusata ne da wani samamen da ‘yan sandan Isra’ila suka kai masallacin Al Aqsa a ranar Laraba.

Wasu hotunan bidiyo ma dai sun nuno yadda ‘yan sandan na Isra’ila ke gallaza wa wadanda suka samu suna gudanar da ibada a masallacin.

Su dai jami’an na Isra’ila sun ce sun kai samamen ne saboda katarin da bikin Passover na Yahudawa ya yi da ibadun da Musulmai ke karfafawa a wannan wata na Ramadana.

Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like