Isra’ila ta shirya yin sulhu da Falasdinawa


Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas da fira ministan isra’ila Benjamin Netanyahu a birnin Washington

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce, a shirye kasar take ta zauna a taburin sulhu don kawo karshen rikici tsakaninta da Falasdinawa, sai dai ba za ta amince da duk wata barazanar wanzuwar kasad ba.
Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta amince da kafuwar kasar a shekara mai zuwa, lokacin da ake cika shekaru 100 da janyewar Birtaniya a yankunansu da kuma kafa mulkin Yahudawa.

A yayin da yake jawabi, Mahmud Abbas ya shaida wa taron Majalisar Dinkin Duniyar cewa, shirin Isra’ila na fadada gine-ginenta a yankin yamma da kogin Jordan na bayar da gudunmawa wajen dakushe fatan samun zaman lafiya tsakanin Falasdinawa da Isra’ila.

Shugaba Abbas ya kuma bukaci taron kasashen na zauren Majalisar Dinkin Duniyar da ya amince da kafuwar kasar Faladinawa mai cikakken ‘yanci.

Sai dai a martaninsa, Netanyahu ya ce, batun fadada gine-ginen Yahudawa ba shi da alaka a rikicin da yake ci gaba da barkewa, abin yi shi ne, Falasdinawa su ajiye makamai.

Wani rahoto da kungiyar Tarayyar Turai da Rasha da Amurka da kuma Majalisar Dinkin Duniya suka fitar ya ce, gine-ginen da Isra’ila ke yi a yankin Falasdinu na barazana ga samun zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu.

You may also like