Ivory Coast : Ana Cikin Zaman Dar-dar A Bouake


 

Rahotanni daga kasar Ivory Coast na cewa ana cikin zamen dar-dar a birnin Bouake a yayin da sojoji ke ci gaba da yin bore na neman a kara musu albashi da kuma wasu alawus alawus.

Bayanai daga kasar sun ce bore ya bazu a wasu birane biyar na kasar, yayin da ake sa ran ministan tsaron kasar zai ziyarci yankin na Bouake domin kwantar da hankali.

A jiya ne dai sojojin wadanda tsaffin yan tawayen da aka shigar dasu aikin soji ne suka toshe wasu tituna na birnin  bayan da suka farmawa wasu offishin ‘yan sanda suka kwashi bindigogi da motoci.

koda a safiyar nan ma rahotanni sun ce an jiyo karen harbe harben mayan bindigogi bayan da suka shafe daren jiya suna ta harbe harben.

You may also like