
Asalin hoton, Getty Images
Ivory Coast ta ci Gambia 2-0, a wasa na bibiyu a rukuni na shida don neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a 2024.
Daf da za su je hutu ne Ivory Coast ta ci kwallo ta hannun Christian Kouame, sannan ta kara na biyu saura minti hutu a tashi ta hannun Seko Fofana.
Da wannan sakamako, Ivory Coast wadda za ta karbi bakuncin gasar cin kofin nahiyar Afirka a 2024, tana ta daya a rukuni na shida da maki shida.
Gabon ma maki shida ne da ita, wadda aka bai wa tazarar rarar kwallaye, bayan da Ivory Coasr ta durawa Seychelles 9-0 a wasan farko a cikin rukuni ranar Juma’a.
Ita ma Equatorial Guinea ta yi nasara a wasa biyu na cikin rukuni, ita kuwa Guinea-Bissau ta ci wasan farko na cikin rukuni bayan fafatawa biyu.
Equatorial Guinea ta je ta doke Liberia 1-0, kuma tsohon dan wasan Middlesbrough da Birmingham City, Emilio Nsue ne ya ci mata kwallon.
Kenan Equatorial Guinea, wadda ta yi wasa biyu, tana ta daya a rukuni na takwas da tazarar maki uku tsakaninta da Tunisia da Malawi, wadanda za su kece raini a tsakaninsu gobe Talata.
Ita kuwa Guinea Bissau nasara ta yi 1-0 a kan Djibouti a Masar, duk da an korar mata mai tsaron baya, Houboulang Mendes, saura minti takwas a tashi daga fafatawar.
Mauro Rodrigues ne ya ci mata kwallon, yanzu tana da maki shida a matakin farko da tazarar maki biyu tsakaninta da Masar.
Tawaga tara ce za ta wakilci Afirka a gasar kofin duniya da za a yi a 2026 a Amurka da Mexico da Canada, kenan duk wadda ta ja ragamar kowanne rukuni ita ce za ta wakilci Afirka.