Ivory Coast ta lashe kofin Afirka bayan cin Najeriya.

Asalin hoton, getty images

Ivory Coast ta lashe kofin Afirka na bana, bayan cin Najeriya 2-1 a wasan karshe ranar Lahadi.

Ivory Coast ce ta karbi bakuncin gasa ta 34 a babban wasannin tamaula na Afirka, wadda ta lashe kofin karo na uku a tarihi.

Super Eagles ce ta fara cin kwallo ta hannu William Troost-Ekong saura minti takwas su je hutun rabin lokaci.

Franck Kessie ne ya farke kwallo daga bugun kwana da Adingra ya buga, hakan ya sa wasan ya koma 1-1.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like