Iyalan Buhari sun Nesanta Kansu Daga wasu Hotunan Bikin Zahra



Iyalan Shugaban Kasa, Muhammad Buhari sun nesanta kansu da wasu hotunan shirye shiryen bikin diyar su, Zahra Buhari da angonta, Ibrahim Indimi wanda ake yadawa a cikin shafukan Sada zumunta na zamani.
Da yake karin haske kan batun, Mai Ba Uwargidan Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Yada Labarai, Adebisi Olumide-Ajayi ya ce wadannan hotuna sun kunyata iyalan Shugaban kasa inda ya kara da cewa da zarar lokacin bikin ya karato, za a fitar da sahihan hotuna dangane da bikin auren.

You may also like