Iyalan Tsohon Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, Kanal Sambo Dasuki sun nemi gwamnatin tarayya ta sake shi.
Iyalan sun yi wannan kiran ne a karkashin kungiyar Sultan Ibrahim Dasuki a lokacin da suke juyayin cika shekaru biya da ci gaba da tsare dan uwan nasu bisa zargin karkatar da kudaden makamai.