Rahotanni daga sassan kasar Somalia dake fama da yunwa sun nuna cewa matsalar tayi kamarin da a halin yanzu, iyaye zaben yaran da zasu bai wa abinda zasu ci su ke yi, saboda rashin abincin.
Fatuma Abdille, wata uwa da ta tsallake rijiya da baya, wajen isa birnin Mogadishu da yaran ta 7, tace dan abinda suka samu, su kan duba yaron da yafi bukatar abincin su bashi, sauran kuma su hakura.