Iyayen yaran aka sace a Zamfara sun nuna fargaba kan makomar ‘ya’yansu'Yan bindiga

Asalin hoton, OTHER

A jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya, iyayen yaran da aka sace na can na nuna fargaba kan makomar ‘ya’yansu.

Rahotanni sun ce wasu ‘yan bindiga ne suka afka kauyen Wanzamai da ke karamar hukumar Tsafe da safiyar ranar Jumma’a inda suka yi awon gaba da yaran.

Wani mazaunin kauyen da BBC ta tattauna da shi ya ce, yawancin yaran da aka sace matasa ne ‘yan tsakanin shekaru sha wani abu zuwa 20 da haihuwa.

Kuma ‘yan bindigar sun afka musu ne bayan da suka je neman itace da kuma gyaran gona.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like