Hukumar ‘yan sandan jihar Ogun sun cigaba da tsare Joe Fortomose Chinakwe wanda ya sanyawa karensa suna Buhari a kurkuku.
Rundunar ‘yan sandan jihar ce dai ta gurfanar da Joe Fortomose Chinakwe a gaban kotun majistare a jiya Litinin, bisa zargin shirin tada zaune tsaye, sakamakon yawon da yake yi da karen sa, wanda ya rubuta sunan Buhari a sassan jikin karen.
Jim kadan, kotun dai ta bada belinsa, to sai dai bai cika sharudan beli ba, dan haka aka ci gaba da tsare shi a gidan kaso.