Izala Tayi Jana’izar Mahaifiyar Dr. Isah Ali Ibrahim Pantami Shugaban Ƙungiyar Izala ta kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya kadu kwarai tare da jimamin rasuwar Shugaban Izala ta karamar hukumar Gombe, Alh. Abdullahi Ɗan Musa, tare da Dottijuwa Mahaifiya ga Sheikh Dr. Isa Ali Pantami, Wanda take unguwar Pantami duka a cikin garin Gombe, kuma a rana daya.

Sheikh Bala Lau yace farko yana mika ta’aziyya ga ‘yay’an marigayan, tare da addu’ar Allah ya jikansu da rahama, ya kyautata bakwancinsu, ya albarkaci abun da suka bari a baya.

Shugaban yace Rashi irin na Shugaba Dan Musa, Babban rashi ne a kasa baki daya, kasancewar yana jagorancin Karamar hukumar Gombe ne, amma alkhairan sa ya kewaye duk fadin ƙasar nan, mutum ne mai kokari wajen hidima wa addini, tare da jajircewa ba dare ba rana akan abun da ya shafi aikin Allah, Muna masa kyakkyawan zato na alkairi, tare da fatan Allah ya hadamu a gidan Aljanna firdausi ranar gobe kiyama.

Sheikh Lau ya kara da cewa itama Mahaifiya ga Shehin Malami Dr. Isa Ali Pantami, wacce da addu’ar ta Malamin ya taso har ya zama abun da ya zama, Na shahara a duniyar Ilimi, muna mata addu’ar Allah ya amshi baƙuncinta, ya baiwa Malam Isa Ali hakurin rashi, ya hadamu a jannatul Firdausi baki daya. Amin.

You may also like