Shugaban Kungiyar Izala na kasa Sheikh Bala Lau ya bayyana haka ne cikin jawabinsa ga ‘ya’yan kungiyar a wajen babban Wa’azin kasa na kungiyar a Jihar Kano. Sheikh Bala Lau, yace “Yan izala cikinsu har da SAN sun zo sun same shi, sun ce da shi zasu tsaya masa da kungiyar kyauta ba ta re da an basu sisin kwabo ba, don gurfanar da Sheikh Dahiru Bauchi, a gaban shari’ah akan cewa Bala Lau, ya nemi hadin kan yan Dariku don a yaki yan shi’ah a Nigeriya” Sheikh Bala Lau ya ce bai taba neman hadin kan yan Dariku ba, don a yaki shi’ah don haka karya Sheikh Dahiru Bauchi yayi musu don haka zai amsa kiran kotu.