Jagoran ƴan adawar ƙasar Kenya ya rantsar da kansa a matsayin shugaban ƙasa.
An tsaurara matakan tsaro a Nairobi babban birnin ƙasar yayin da gwamnati ta rufe gidajen Talabijin masu zaman kansu domin hana su nuna bikin rantsuwar.
A ranar Litinin Linus Kaikai shugaban ƙungiyar Editoci ta ƙasar, yace jami’an tsaro sun gayyaci manyan editoci inda aka gargade su kada su nuna taron ko kuma su fuskanci fushin hukuma da ya hada da rufe kafafen yaɗa labaran da suke wa aiki.
Odinga mai shekaru 72 ya yi farin ciki lokacin da kotu ta soke nasarar zaɓen da shugaba, Uhuru Kenyatta ya samu amma kuma yaƙi shiga zaɓen da aka yi a karo na biyu inda ya zargi gwamnati da shirya magudi.
Kenyatta ya lashe zaɓen da kaso 98 cikin ɗari.
Jagoran ƴan adawar wanda a baya ya sha dage ranar da zai rantsar da kansa amma a wannan karon jam’iyar sa ta dage kan cewa sai bikin ya gudana.