Jagoran ‘yan ta’addan IS, Abou Bakr al-Baghdadi, ya kira mayakansa dasu ci gaba da rike Mosul a daidai lokacin da dakarun Iraki ke luguden wuta a cikin birnin dake zamen tunga ta karshe ta ‘yan ta’addan ke rikeda.
A cikin wani sako da kafar yada labarai ta Al’Furqan ta watsa an jiwo wata murya da aka ce ta al-Baghdadi ce tana kira ga mayakanta su kimanin 3,000 zuwa 5,000 dasu ci gaba da jan daga a birnin na Mosul.
Wannan dai shi ne karon farko a cikin sama da shekara guda da a ji muryar al-Baghdadi wanda aka jima ana kace nace akan halin da yake ciki.
A halin da ake ciki dai dakarun gwamnatin Iraki sun kutsa cikin birnin na Mosul, wanda a karon farko tun bayan da kungiyar da karbe shi shekaru biyu da suka gabata, sun ce za su ci gaba da dannawa cikinsa har sai baki dayansa ya dawo karkashin ikon gwamnati.
Mai magana da yawun sojojin Iarakin Sabah al-Numan, ya shaidawa masu aiko da rahotanni cewa a yanzu dakarun su a shirye suke dan fara yakin ta hanyar binciken kowannen gida.