Jagororin Jam’iyyar PDP Za Su Gurfana A Gaban Kotu A Yau


Ana sa ran yau da misalin karfe biyu na rana, tsohon Gwamnan jihar Kano Dakta Malam Ibrahim Shekarau da kuma Ambasada Aminu Wali da Injiniya Mansur Ahmed wanda shine mataimakin shugaban yakin neman zaben tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan a yankin Arewa.

Ana zargin jagororin jam’iyyar da kalmashe Naira Miliyan 950m Na Yakin Neman Zaben Jonathan a 2019.

A baya hukumar EFCC ta gayyaci Aminu Wali inda ya amsa karbar Naira Miliyan 25 wanda yayi ikirarin sun raba kudin a gidan Shekarau. Wannan ya sa Shekarau ya kai kansa ga EFCC tare da amincewa da an raba kudin a gidan sa, amma bai karba ba. Wanda hakan ya janyo sanadiyyar tsare shi na tsawon kwanaki uku tare da zuwa bincike gidansa da Jami’an tsaro.

You may also like