Jahilci Ke Janyo Wasu Ke Kisa Da Sunan Addini – Buhari Shugaba Muhammad Buhari ya jaddada cewa jahilci ne ka janyo wasu ke zubar da jinin ‘yan uwansu da sunan addini inda ya yi alwashin hukunta duk wadanda ke da hannu wajen kisan kai a duk fadin kasar nan.

Buhari ya yi wannan ikirarin ne a lokacin da ya karbi bakuncin Shugabannin kungiyar Izala a karkashin jagorancin Sheik Bala Lau da kuma shugabannin kungiyar Darikar Kadiriyya ta Afrika a fadarsa da ke Abuja. Ya ce babu yadda za a kashe rai don a farantawa Ubangiji.

You may also like