Shugaban Rundunar Sojan kasa, Janar Tukur Burutai ya tabbatar da cewa yadda mayakan Boko Haram ke ci gaba da kai hare hare na daurewa rundunar Sojan kai ganin an ci galabarsu a cikin Dajin Sambisa.
Burutai ya nuna cewa mayakan kungiyar da aka kama a halin yanzu duk yunwa ta ci karfinsu sannan kuma duk an dakile hanyoyin da kungiyar ke samun taimako amma kuma hakan bai sa sauran mayakan kungiyar daina kai jerin hare hare ba.
Ya kara da cewa wani abu da ya kara ba su mamaki game da kungiyar shi ne kafin su arce daga hedkwatarsu da ke cikin Sambisa sai da suka kai hari ga sojoji ta hanyar amfani da wata tankar yaki wadda suka dora mata bama bamai. Ya ce rundunar na ci gaba da bincike bisa yadda mayakan kungiyar suka lakanci sarrafa irin wadannan manya tankokin yakin.