Jami’an Ƴansanda Sun Buɗe Wuta Kan Mabiya Shi’a Masu Zanga-Zanga A Kaduna


 

Zakzaky-shiites-1

Ƴansanda a kaduna a yau talata sunyi harbi kan mabiya mazhabar shi’a wadanda suke gudanar da zanga- zangar lumana ta neman a sako jagoransu Sheikh Ibrahim Zakzaky,wanda suka ce ana tsare dashi ba bisa ka’ida ba.
Yan Kungiyar ta shi’a sun bi sahun dubban takwarorinsu da suke garuruwa da dama a arewacin Najeriya wajen gudanar da zanga zangar lumana kan an sako,jagoran nasu. Wanda ake cigaba da tsare shi duk da umarnin da Kotu ta bayar na a sake shi.
Jerin gwanon masu zanga-zangar ya fara lafiya a kan hanyar Nmandi Azikiwe Western Bye pass.amma suna isa mahadar hanya ta Bakin Ruwa sai sukaci karo da jami’an Yan sanda dauke da makamai inda suka bude musu wuta har takai ga raunata wasu Yan kungiyar.
Shedar gani da ido yace Yan sanda sun gayyaci Yan daba da kuma Bata gari,kamar yadda suka Saba a baya bayannan wajen Kai hari kan Yan kungiyar.
An dai dakatar da zanga -zangar ta lumanar kafin rikicin ya tsamari.Shugabannin kungiyar sun nuna rashin Jin dadinsu kan yadda yansanda sukayi amfani da karfin tuwo kan Yankasa da suke gudanar da hakkin da kundin tsarin mulki yabasu.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like