Jami’an Ƴan Sanda Na Gayyatar Saraki Kan Ya Yi Bayani Kan Alaƙar Sa da Ƴan. Fashi


Rundunar yan sandan Najeriya ta gayyaci Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki domin amsa tambayoyi kan wasu yan fashi da makami da suka ce suna da alaka da shi.

Kakakin yan sandan Jimoh Moshood yace 5 daga cikin yan fashi 22 da aka kama sakamakon kazamin fashin da akayi a Offa wanda yayi sanadiyar kashe mutane 17 cikin su harda Yan Sanda 9, sun bayyana alakar su da shugaban Majalisar Dattawan.

Moshood yace wannan ya sa rundunar yan sandan ta gayyace shi domin yin bayani kan alakar sa da yan fashin.

Makwanni 3 da suka gabata, Sanata Bukola Saraki yayi zargin cewar Rundunar na shirin bata masa suna, bayan ta kwaso wasu yan fashi daga Jihar kwara zuwa Abuja, abinda ya sa Majalisar Dattawa ta tura wakilai domin ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

You may also like