Hukumar kare fararen hula wato ‘Civil Defence’ reshen jihar Borno, a safiyar yau Talata sun yi nasarar dakile wani yunkurin kai hari da wasu mata ‘yan kunan bakin wake guda biyu suka so kaiwa cikin jerin motocin dake dauke da jama’a a daidai NNPC Mega Station dake kusa da titin Damboa a garin Maiduguri babban birnin jihar.
Kwamandan hukumar, Ibrahim Abdullahi, ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) cewa lamarin ya auku ne da misalin karfe 6.45 na safiyar yau Talata.