Jami’an Diflomasiyyar Amurka Sun Gana Da Hukumar Zaben NajeriyaABUJA, NIGERIA – Hukumar kuma ta ce cikin adadin tuni sun gudanar da guda goma sha biyu.

Amurka ta kara bayyana sha’awarta game da hada hadar tsarin dimokradyyar Najeriya tare da jaddada kiranta na a gudanar da zabuka cikin kwanciyar hankali da lumana, bisa tsarin gaskiya da adalci.

Mataimakiyar Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Uwargida Molly Phee, wacce a halin yanzu ke ziyarar aiki a Najeriya, ita ce ke bayyana haka yayin da ta jagoranci jami’an Diflomassiyar kasarta wajen ganawa da hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya a Abuja.

Jami’an Diflomasiyyar Amurka Sun Gana Da Hukumar Zaben Najeriya

Jami’an Diflomasiyyar Amurka Sun Gana Da Hukumar Zaben Najeriya

Baya ga nuna shaukin gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali, mataimakiyar sakataren harkokin wajen Amurkan din ta kuma yi amannar cewa za a kare martabar tsarin demokraddiya kamar dai yadda aka assasa tun daga shekara ta 1999 kawo yanzu.

Uwargida Molly Phee ta jaddada cewa akwai wani alhaki da ya rataya a wuyan kowane dan Najeriya, yan siyasa, jami’an zabe da na gwamnati da ma sauran masu ruwa da tsaki na su tabbatar da cewa kafin lokacin zabe da kuma bayan zaben an yi abin da ya kamata cikin tsanaki da sanin ya kamata, kamar dai yadda aka tsara.

Jami’an Diflomasiyyar Amurka Sun Gana Da Hukumar Zaben Najeriya

Jami’an Diflomasiyyar Amurka Sun Gana Da Hukumar Zaben Najeriya

Tunda farko, shugaban hukumar zaben Najeriya, Farfesa mahmoud yakubu, ya bayyana cewa hukumar zaben Najeriyar a shirye take wajen tabbatar da dorewar nasarar tsarin demokradiyya.

Yana mai cewa INEC, tun a watan fabrairun shekarar bara, ta fidda jadawalin babban zaben inda ta ayyana wasu muhimman ababe guda goma sha hudu da bisa doka dole sai an gudanar dasu, inda yace cikin wannan adadin sun sami nasarar gudanar da guda goma sha biyu.

Farfesa mahmoud Yakubu ya ce a halin yanzu ababe biyu ne kacal ya rage masu wato rufe gangamin yakin neman zabe da za a kawo karshensa ranar Alhamis, ashirin da uku ga watannan na fabrairu, sai kuma ranakun zabe a matakan tarayya da na jihohi.

Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina:Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like