Jami’an EFFC Sun Kai Sumame Gidan Tsohon Gwamnan Jihar Anambra Peter Obi


Peter Obi

Valentine Obienyen mai taimakawa tsohon gwamnan jihar Anambra Mista Peter Obi kan kafofin yaɗa labarai yace jami’an hukumar yaƙi da yiwa tattalin arzkikin ƙasa ta’annati, EFFC sun kai sumame gidan tsohon gwamnan bayan da aka gano $43 a kusa da gidan da yake zaune a Legas.

A wata sanarwa Obienyem yace Obi da matarsa sun karbi hayar gidan da aka kai sumamen kuma suna zama a ciki a duk lokacin da sukaje birnin Legas.

Yaƙara da cewa lokacin da aka kai sumamen tsohon gwamnan bayanan yana can ƙasar Amurka tare da matarsa.

“Duk da tsohon gwamnan da matarsa sunyi tafiya zuwa ƙasashen Amurka da Birtaniya don gabatar da wasu maƙaloli  da muka faɗa masa batun binciken  na EFCC, yayi gaggawar turo da maƙullan gidan ta hanyar kamfanin aikawa da saƙonni zuwa ga EFCC”sanarwar tace

“ Ya kuma bada umarni da mu basu damar su bincika gidansa dake birnin Onica idan suna da buƙata, bayan cikakken bincike babu abun da aka samu a gidan”

You may also like