Jami’an Hukumar EFCC Sun Kama Kwamishinan Kudi Na Jihar Ekiti  


Hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC, ta kama Toyin Ojo, kwamishinan kudi na jihar Ekiti da kuma babban akanta na jihar. 

Jami’an hukumar sun kama mutanen ne jiya Alhamis a babban birnin jihar Ado-Ekiti.

Wilson Uwujaren, mai magana da yawun hukumar yace an kama jami’an gwamnatin ne bayan da suka gaza amsa gayyatar hukumar na su bayyana a gabanta. 

“yanzu haka suna tsare a hannun mu  an kama sune  a yau bayan da suka ki girmama gayyatar da akayi musu zuwa hukumar don su amsa tambayoyi kan yadda gwamna Ayo Fayose ya barnatar da kudaden biyan bashin kudin Paris Club, “yace. 

An kama jami’an ne a dai-dai lokacin da lokacin da Fayose yake neman tsayawa takarar shugaban kasa. 

  Duk da cewa jam’iyar PDP ta bayyana cewa dan takarar jam’iyar na shugaban kasa zai fito ne daga arewacin Najeriya hakan bai sa Fayose daina kwadayin zama shugaban kasa ba. 

You may also like