Jami’an hukumar Yaki Da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati,EFCC sun yi awon gaba da tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shehu Shema, bayan da wata kotun tarayya ta bada umarnin a tsare shi.
Kotun ta yanke hukuncin cewa a cigaba da tsare tsohon gwamnan a hannun hukumar EFCC har ya zuwa ranar 27 ga watan Afirilu inda za ta cigaba da zama ta kuma saurari batun beli da tsohon gwamnan ya nema.
Jim kadan bayan yanke hukuncin jami’an hukumar ta EFFC da saura jami’an tsaro sun kewaye harabar kotun ya yin da magoya bayansa suka taru rukuni-rukuni suna tattauna hukuncin kotun.
Daga baya wajen misalin karfe 5:53 an saka sheka Shema a cikin wata mota kirar Toyota mai cin mutane 18 inda aka wuce da shi ya zuwa ofishin hukumar dake Kano .
A cikin motar akwai jami’an hukumar EFCC da kuma shugaban jam’iyar PDP na jihar Katsina Alhaji Salisu Maijigiri.