Jami’an Hukumar SSS Sun Kama ‘Yan Ta’addan Boko Haram A Kano


4bk3d7b9642ef14n01_800c450

Hukumar jami’an tsaron farin kaya ta Nijeriya (SSS) ta sanar da samun nasarar kame wasu mutane uku da ake zargin cewa mayakan kungiyar ta’addancin nan ta Boko Haram ne a kauyen Dirbunde da ke karamar hukumar Takai da ke jihar Kano ta Nijeriyan.

Hukumar SSS din ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar dauke da sanya hannun daya daga cikin jami’anta mai suna Tony Opuiyo inda ya ce mutane ukun da aka kama din wato Samaila Muhammad, Sanusi Musa da kuma Hudu Muhammad suna kulle-kullen kai wasu hare-hare da ababe masu fashewar a wasu jihohi na arewa maso yammacin Nijeriya din ne.

Har ila yau sanarwar ta kara da cewa jami’an SSS din sun sami nasarar kame wasu da ake zargin ‘yan ta’adda su biyu, wato Sani Digaru da Mohammed Ali  a ranar 25 ga watan Disambar nan a kan hanyar Gombe-Dukku , da ke jihar Gombe ta Nijeriya. Sanarwar ta kara da cewa jami’an tsaron sun harbi Sani Digaru din a lokacin da yayi kokarin gudu. Sanarwar ta ce sun kama mutanen ne bayan da suka sami wani labari na sirrin cewa mutane suna dauke da kudin da suka kai Naira miliyan biyu da ake shirin amfani da su wajen ayyukan ta’addanci a jihohin Yobe da Bauchi.

Har ila yau hukumar SSS din ta ce ta sami nasarar ganowa da kuma kame gungun ‘yan wata kungiya ta mutanen da suka kware wajen fashi da makami wa baki ‘yan kasashen wajen a birnin Abuja, babban birnin Tarayyar Nijeriyan.

You may also like