Jami’an INEC Sun Jibge Takardun Yiwa Melaye Kiranye A Bakin Ofishinsa 


Hukumar Zabe Ta Kasa INEC ta jibge tarin takardun yiwa sanata Dino Melaye, dake wakiltar mazabar Kogi ta yamma kiranye a bakin ofishinsa dake ginin majalisar tarayya.

Tarin takardun dake makare cikin jakar ‘Ghana Must Go’guda hudu an ajiye su a bakin ofishin da misalin karfe 11:00 na safe. 

Ofishin Melaye dake a bene hawa na biyu na ginin majalisar a garkame yake da kwado lokacin da jami’an hukumar ta INEC suka je domin su damka masa takardun.

 

Tun a baya hukumar ta INEC ta koka kan yadda Melaye yake gudun karbar takardun zargin da Melaye ya sha musaltawa 

You may also like