Jami’an Kwastam sun kama motocin Dangote 2 makare da shinkafar kasar waje


Hukumar Kwastam dake kula da shiyar Sokoto ta kama motocin ɗaukar kaya mallakar rukunin kamfanonin Dangote makare da shinkafa mai nauyin 50kg da yawanta ya kai buhu 365.

Lokacin da yake duba kayan da aka haramta shigo dasu, kwantirola dake kula da yankin Nasiru Ahmad ya ce an samu nasarar kama kayan ne saboda sa idon da jami’an sa suke sintiri kan iyaka a hanyar Sokoto zuwa Ilella.

A cewarsa mutum daya da ake zargi aka kama kuma zai fuskanci a da zarar an kammala bincike.

“Dukkan mu mun san cewa gwamnatin tarayya ta hana shigo da shinkafar ƙasar waje ta kan iyakoki kasa, abin da suka aikata ya sabawa tsarin gwamnatin tarayya kan shinkafa wanda babban laifine,” yace .

Ahmad ya kara da cewa:”Tabbas zamu hukunta ko waye yake da hannu a fasa kwaurin shinkafar.”

You may also like