Jami’an Kwastan Sun Harbe shi Bayan Ya Yi Safarar Shinkafa Daga Nijar Zai Shigo Da Ita Najeriya


Ina mai amfani da wannan dama wajen yin Allah wadai da wannan danyen hukunci da jami’an kwastam masu sintiri a shingen mashigar karamar hukumar mulki ta Gwadabawa.

Jami’an sun harbe wannan direba ne mai suna Sha’aibu bayan ya yiwo fasa kwafrin shinkafa daga Jamhoriyar Niger ta kan iyakar Ilelah dake jihar Sokoto. Bayan sun tsare shi ya ki tsayuwa shine suka bi shi kana daya daga cikin jami’an kwastom din ya harbe shi a goshi inda nan take ya mutu. Wanda aikata hakan yana nunawa rashin iya gudanar da aiki daga wadannan jami’an kwastan, kana hakan na dada tabbatarwa cewa a kullum wadanda ba su cancanci aikin ba ne ake ba su wannan aiki don daurin gindi.

Me ya sa mafi yawancin jami’an tsaron Nijeriya ba sa daukar ran dan adam a bakin komai?

Me ya sa ba za a harbi tayar motar wannan direba ba a maimakon harbin sa?

Hakan na nufin hukuncin duk wanda ya yi fasa kwafri aka tsare shi ya ki tsayawa kenan?

Shin wannan hukunci ya yi dai-dai da tanade-tanaden dokar kwastan da na kasa kenan?

Shin menene matsayin gawar wannan bawan Allah a halin yanzu?

A karshe muna kira ga hukumar kwastan kan lallai ta biya diyya(damage compensation) ga iyalan wannan direba kuma a hukunta wanda ya yi wannan harbi nan take.

Muna kuma kira ga jama’a kan su zama masu kiyaye doka don gujewa wulakanci tare da kisan gilla irin na wannan bawan Allah. Hakan ne kawai zai sa a samu ci gaba mai dorewa.

You may also like